
A cewar Euronews, gwamnan jihar Florida Ron DeSantis ya bayar da umarnin zartarwa inda ya ayyana kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma majalisar huldar Amurka da Musulunci ta CAIR, babbar kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda na kasashen waje. Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnan jihar Texas ya yanke irin wannan hukunci.
Umurnin zartarwa wanda DeSantis ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X a ranar Litinin, ya bayyana cewa kungiyoyin biyu na da alaka da kungiyoyin da ke adawa da Isra'ila da suka hada da Hamas, Hezbollah da sauran kungiyoyin Falasdinu.
Ya kuma umurci hukumomin jihar da su ki bayar da kwangila, kudade ko duk wata alfarmar gwamnati ga mutanen da suka ba da tallafin kayan aiki ga kungiyoyin biyu.
Majalisar kula da huldar muslunci ta Amurka reshen jihar Florida da ofishinta na kasa ta fitar da sanarwar hadin gwiwa a ranar Talatar da ta gabata inda suka bayyana matakin da ya sabawa ka'ida kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, inda suka sanar da cewa nan ba da jimawa ba za su shigar da kara a gaban kotun tarayya. Majalisar hulda da muslunci ta Amurka, ta kuma yi ishara da wani mataki makamancin haka da gwamnan jihar Texas, Greg Abbott ya yi, inda ya bayyana gwamnonin biyu a matsayin 'yan siyasar Isra'ila, ya kuma bayyana cewa, sanya majalisar a matsayin 'yan ta'adda, an yi shi ne domin rufe bakin bakin Amurkawa, musamman musulmin kasar, wadanda ke sukar irin goyon bayan da Amurka ke yi na aikata laifukan yaki na Isra'ila.