
cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na alwihdainfo cewa, a jiya kwamitin kare hakkin bil adama a kasar Chadi ya yi kakkausar suka dangane da kisan musulmi da ake yi a akasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya ba gaira ba sabar, tare da bayyana hakan a matsayin aikin ta'addanci mafi muni a bayan kasa.
A nasa bangaren shugaban Kasar chadi Idris Deby ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Afrika ta tsakiya. Shugaba Idris Deby da shi ne shugaban kasa a nahiyar Afrika na farko wanda ya yi wannan irin kiran, yana kuma son ganin cewa rundunar da za a kafa ta yi aiki tukuru domin dawo da zaman lafiya mai dorewa a cikin Afrika ta tsakiya. Kiran na shugaban Kasar Chadi ya zo ne a daidai lokacin da kasar ta Afirka ta tsakiya ta ke ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula kuma kasashen Faransa da wasu daga nahiyar Afirka su ka girke sojojinsu a cikinta.
Har ila yau shugaban kasar ta Chadi ya kuma yi gargadi akan yiyuwar darewar wannan kasa gida biyu, idan har ba a kawo karshen rikicin da ya ke faruwa ba. A wani labarin na daban, an bayyana cewa fiye da musulmin kasar 2000 ne suka tsallaka iyaka zuwa kasar Kamaru a cikin kwanakin bayan nan. Jaridar Yaumu assabii, ta ce kawo ya zuwa yanzu adadin muuslmin da su ka ketara iyaka sun kai 20,000.
An kai hare-haren ta’addanci na kunar bakin wake a birnin Beirut na kasar Lebanon a yau laraba. Rahotannin da su ke fitowa daga kasar Lebanon sun ce wasu ‘yan kunar bakin wake biyu sun kai harin ta’addanci a cikin unugwar da ke kudancin Beirut wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 4 da jikkata wasu da dama.
Daya daga cikin harin dai an kai shi ne a kusa da karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma ofishin kamfanin Dillancin Labarun Irna da ke birnin Na Beirut. Tuni jami’an gwamnatin Lebanon su ka fara yin Allah wadai da kai harin tare da yin kira da a dauki matakan da su ka dace domin kalubalantar ‘yan ta’adda.