IQNA

Ana Saka Guba A Cikin Abincin Da Musulmi Suke Ci A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

17:55 - April 09, 2014
Lambar Labari: 1392670
Bangaren kasa da kasa, a wani sabon salo a kasashe musulmi bayan kisan da ake yi musu da wuka da bindigogi da adduna a jamhuriyar Afirka ta tsakiya an gano cewa a halin yanzu ana saka guba a cikin abincin da suke ci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na rfi.fr cewa, wani sabon salo a kasashe musulmi bayan kisan da ake yi musu da wuka da bindigogi da adduna a jamhuriyar Afirka ta tsakiya an gano cewa a halin yanzu ana saka guba a cikin abincin da suke ci domin kawai a halaka su.
Harin wuce gona da iri na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ‘yan dabar kiristoci ta Anti-Baleka suka kai kan al’ummar musulmi da suke gudanar da jana’izar mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin ta’addanci da kiristoci masu dauke da makamai suka kai kan yankin Fatima da ke gefen birnin Bangui fadar mulkin kasar, inda harin ya lashe rayukan mutane akalla 20 tare da jikkata wasu da dama.
Sakamakon bakar aniyar ‘yan dabar ta kiristocin kungiyar Anti-Baleka na kokarin kawo karshen al’ummar musulmin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta hanyar kai musu jerin hare-haren wuce gona da iri a kusan kullum rana; babban kwamandar dakarun wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Janar Jean-Marie Michel Makoko a ranar Larabar da ta gabata ya fito fili ya jaddada cewar dakarunsa zasu ci gaba da kalubalantar mayakan kungiyar ‘yan dabar kiristoci ta Anti-Baleka a matsayin makiya.
Har ila yau Janar Makoko ya yi furuci da cewa; Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa da mafi yawansu sun fito ne daga kasashen nahiyar Afrika gami da sojojin kasar Faransa 2000 da a jimila dakarun na kasa da kasa suka kai kimanin dubu shida, tabbas ba zasu iya shawo kan hare-haren wuce gona da iri da ‘yan dabar kungiyar kiristoci ta Anti-Baleka ke kai wa kan yankuna daban daban na kasar ba.
1391805

Abubuwan Da Ya Shafa: afirka
captcha