IQNA

Gwamnatin Tunisia Ta Kwace Masallatai 15 Daga Hannun 'Yan Salafiyyah

18:02 - April 09, 2014
Lambar Labari: 1392672
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Tunisia sun fara daukar matakai na shiga kafar wando daya da masu dauke da mummunar akidar nan ta salafiyya da ke kafirta al'ummar musulmi inda yanzu haka aka kwace masallatai goma sha biyar daga hannunsu domin taka musu birki. Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa,

ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo huffpostmaghareb cewa, yanzu haka mahukuntan kasar Tunisia sun fara daukar matakai na shiga kafar wando daya da masu dauke da mummunar akidar nan ta salafiyya da ke kafirta al'ummar musulmi inda yanzu haka aka kwace masallatai goma sha biyar daga hannunsu domin taka musu birki kan ayyukan wuce gonad a iri da tayar da fitina da suke yi.

Daya daga cikin manyan jami'an gwamnatin ta Tunisia Abdulrazaq bin Khalifah ya bayyana cewa, a lokutan baya akwai masallataia fiye da 150 a hannun 'yan salafiyya masu tsatsauran ra'ayio da ke kafirta sauran al'ummar kasar, amma yanzu gwambatin ta yi nasarar kwace kimanin 30 daga cikin wadannan masallatai, kuma za a ci gaba da yin hakan sai an ci karfinsu, da kuma kwo karshen barazanar da suke yi ga zaman lafiyar al'ummar kasar.

Fada ta barke tsakanin yan bindiga da jami’an tsaron kasar Tunisi a kudu masu gabaci da kuma arewacin kasar a safiyar yau litinin wanda ya kai ga mutuwa da kuma raunata mutane da dama Jaridar Asharq ta kasar Qatar ta bayyana cewa, fada tsakanin yan bindigan da kuma jami’an tsaron gwamnati a lardunan
Ya cin ya rayukan yan bindiga da dama ya kuma raunata wasu jami’an tsaro labarin ya kara da cew a safiyar yau litinin, yan bindiga sun kai farmaki kan wani jirgin ruwan jami’an tsaro a lardin  inda suka raunata jami’an tsaro guda biyu haka ma radioyin lardunan biyu sun bada labarin cewa jaragen yaki masu saukar ungulu suna shawagi a kan yankunan biyu.
1391904

Abubuwan Da Ya Shafa: tunis
captcha