
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, yanzu haka , ana shirin far gudanar da babban taron musulmi a kasar Ivory Coast wanda aka saba gudanarwa a kowace shekara tare da halartar manyan malaman addinin Musulunci na kasar da ma wasu daga cikin kasahe makwabta da suka hada da Burkina Faso, Benin da kuma Mali.
A wani labarin kuma Shugabannin kasashen kungiyar raya harkar tattalin arzikin yankin Afrika ta yamma ecowas zasu fara gudanar da zaman taronsu a birnin Yamoussoukro fadar mulkin kasar Ivory Coast a yau Juma’a, kamfanin dillancin labaran ya bayyana cewar za a bude zaman taron shugabannin kasashen kungiyar raya harkar tattalin arzikin yankin Afrika ta yamma ecowas ne a birnin Yamoussoukro fadar mulkin Ivory Coast karkashin jagorancin shugaban kasar Alhasan Watara a yau Juma’a, kuma babban abin da zaman taron zai fi mai da hankali kansa shi ne matsalolin siyasa a kasashen Mali da Guinea Bissau.
Tun daga ranar Talatar da ta gabata ce birnin Yamoussoukro ya fara karbar bakoncin wakilan kasashen kungiyar ta ecowas tare da gudanar da zaman tarurruka kan sharen fagen zaman taron shugabannin kasashen kungiyar ta ecowas kuma daga cikin tarukkan da aka gudanar har da na ministocin tsaron kasashen kungiyar kan matsalolin tsaro da siyasa a kasashen Mali da Guinea Bissau.
1392289