Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawabah Bito cewa, a jiya an nuna wasu alluna da suke dauke da rubutun faaha na musulunci a birnin Alkahira na kasar Masar wanda ma’aikatar kula da harkokin al’adu ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gabatarwa. Wasu rahotanni kuma sun ce dakarun tsaron Masar sun kashe Mutane guda biyu tare da cafke wasu 38 na daban a wani farmaki da suka kai a yankunan Al'arish da Sheihu Zawid Wata majiyar tsaro a kasar Masar ta habarta cewa rundunar hadin gwiwar tsaro ta kasar ta kai wani samame a maboyar 'yan bidiga a anguwar Hayyi Safa dake Garin Al'arish tare da kauyan Mahdiya dake yankin Sheihu Zawid inda suka kashe 'yan bindigar guda biyu Rahoton ya kara da cewa rundunar hadin gwiwar ta samu nasarar kame wasu 'yan bindigar guda 38 sannan kuma ta samu wasu bama-bamai kirar hannu da kuma wasu na'urorin sadarwa tare da wasu bayanan asiri masu nasaba da Dakarun Soja da na 'yan sanda dake arewacin yankin Sina Har ila yau Dakarun tsaro sun bayyana cewa sun samu mashin na hawa guda 31 tare da rusa wasu hanyoyin karkashin kasa guda. 1396260