IQNA

An Zabi Malami Mai dawa Da Akidar Salafiya A matsayin Shugaban Majalisar Malaman Mali

16:02 - April 22, 2014
Lambar Labari: 1398668
Bangaren kasa da kasa, an zabi wani fitaccen malamin addinin muslunci mai adawa da mummunar akidar nan ta salafiyya da ke kafirta sauran al’ummar musulmi a matsayin shugaban majalisar amalaman addinin muslunci ta kasar.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Malijet cewa, gwamnatin kasar ta zabi wani fitaccen malamin addinin muslunci mai adawa da mummunar akidar nan ta salafiyya da ke kafirta sauran al’ummar musulmi a matsayin shugaban majalisar malaman addinin muslunci.
Wannan mataki dai ya zo sakamakon irin tsananin adawar da al’ummar kasar suke nunawa ga bazuwar akidar ta salafiyya wadda mabiyanta suka yi sanadiyyar mayar da kasar baya, bayan kaddamar da hare-haren ta’addanci a cikin yankunan arewacin kasar, sun kuma rusa muhimman wurare na tarihin addinin muslunci da ke kasar.
A WANI LABARIN NA DABAN KUMA Shugaban kasar Mali Ibrahim Bubacar Keita ya shaida cewa jagoran Mayakan jihadi nan Mokhtar Belmokhtar wanda aka bada labarin cewa yana raye kuma yana boye a ksar Libia, babbar barazana ce zaman lafiya.   Shugab Bubacar keita ya shaida hakan ne ga manema labarai a birnin Dakar na kasar Senegal inda yake gudanarda wata ziyara aiki.  
wata Majiyar tsaro a kasar Mali tace Kwamandan Mayakan nan jihadi Mokhtar Belmokhtar da ake nema ruwa a jallo, ya boye a kasar Libya inda ya ke ci gaba da shirya kai hare haren ta’addanci a kasashen yankin Sahel a Afrika. Majiyar ta shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa ta yi imanin Kwamandan wanda ya jagoranci hari a wata cibiyar gas a Algeria kuma wanda ake zargi an kashe a kasar Mali yana buya ne a cikin kasar Libya.
1397866

Abubuwan Da Ya Shafa: mali
captcha