IQNA

An Kammala Wani Zama Na Malaman addinin Musulunci A Kasar Jibouti

10:41 - May 21, 2014
Lambar Labari: 1409190
Bangaren kasa da kasa, an kamala wani zama na malaman addinin mulsunci a gabacin kasar Jibouti da ke gabacin nahiyar Afirka wanda ya tattauna hanyoyin da ya kamata musulmi su bi wajen kyautata surar addinin musulunci.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo French.peopledaily cewa, a jiya an kamala wani zama na malaman addinin mulsunci a gabacin kasar Jibouti da ke gabacin nahiyar Afirka wanda ya tattauna hanyoyin da ya kamata musulmi su bi wajen kyautata surar addinin musulunci bisa la’akari da lamurra da suke faruwa yanzu haka a duniya musulmi.
A wani labarin kuma Gwamatin kasar ta Jibouti ta yi kira ga kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa da su kai taimakon abinci cikin gaggawa a kasar domin taimaka ma wasu daga cikin al'ummar kasar da ke cikin matsanancin yanayi na rashin abin da za su ci. 
Minista mai kula da ayyukan jin kai a kasar ta Jibouti Zahra Yusuf Kaid ita ce ta bayyana hakan a yau, inda ta ce yanzu haka akwai iyalai fiye da 30,000 a kasar da suke bukatar taimakon abinci cikin gaggawa, daga cikin iyalai 147,000 da ake baiwa tallafin abinci a kasar, ta ce tana kira ga kungiyoyin bayar da agaji da suke gudanar da wannan aiki da su kara bayar da himma musamman a wannan lokaci.  
Kasar Jibouti dai na daga cikin kanan kasashe da ke gabacin nahiyar Afirka da ke fuskantar matsalar fari lokaci zuwa lokaci, wanda hakan kan haddasa karancin abinci a kasar, ta yadda sai ta nemi tallafi daga kungiyoyin kasa da kasa domin ciyar da wasu daga cikin iyalai a kasar. 
1408691

Abubuwan Da Ya Shafa: jibouti
captcha