IQNA

Wani Dan Wasan Kwallon Kafa A Birtaniya Ya Karanta Kur'ani A Masallaci

17:29 - May 26, 2014
Lambar Labari: 1411393
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa a kasar Birtaniya da ke wasa a kungiyar kwalo ta Arsenal ya karanta kur'ani mai tsarki a bababn masallacin jum'a a na birnin London a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, wani labari da ya dauki hankula a wannan mako shi ne yadda daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa a kasar Birtaniya da ke wasa a kungiyar kwalo ta Arsenal ya karanta kur'ani mai tsarki a bababn masallacin juma'a a na birnin Landan.

Kafofin sadarwa da dama ta hanyar safukan yanar gizo a Birtaniya, sun nuna hoton bidiyo wanda a cikinsa aka nuna dan wasan kwallon kafa na kungiyar Arsenal Abou Diaby yana zaune a cikin babban masallacin Landan yana karanta surat Nur daga cikin Alkur'ani mai tsarki, wanda hakan ya ja hankulan mutane da dama a kasar.

Dan wasan na Arsenal dai daya ne daga cikin mabiya addinin muslunci da suke buga wasan kewallon kafa a kasar Birtaniya, wanda kuma yana daga cikin masu nuna kishinsa ga addinin muslunci, duk kuwa da irin halin day a samu kansa a ciki, inda akasarin mutanen da yake rayuwa das u ba musulmi ba ne.

1410733

Abubuwan Da Ya Shafa: Diaby
captcha