IQNA

Ayatollah Sistani Ya Kara Jaddada Wajabcin Yaki Da ‘Yan Ta’adda

17:59 - June 22, 2014
Lambar Labari: 1421294
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin Musulunci a kasar Iraki Ayatullahi Aliyu Sistani ya shelanta jihadi kan ‘yan ta’adda da nufin kare kasar daga mamayar ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a hudubar sallar juma’arsa ta yau a birnin Karbala na kasar Iraki Sheikh Abdul-Mahdi Al-Karbala’i wakilin babban malamin addinin Musulunci a Iraki Ayatullahi Sistani ya bayyana cewa; Ayatullahi Aliyu Sistani ya bukaci dukkanin al’ummar Iraki da su daura damara tare da sabar makamai domin yakar ‘yan ta’adda da nufin kare kasar Iraki.
Sheikh Karbala’i ya kara da cewa; Babban hatsari yana barazana ga kasar Iraki don haka wajibi ne a kan mutanen da suke da damar daukar makami su shiga cikin sahun jami’an tsaron Iraki domin kare kasar, kuma duk wanda ya mutum ya yi shahada a matsayin shahidi.
A nashi bangaren Sayyid Muktadha Sadar ya kira yi magoya bayansa da dukkanin al’ummar Iraki da su shiga cikin sahun jami’an tsaron Iraki wajen kare kasar daga babban hatsarin da take fuskanta.
Rahotanni daga kasar Iraki sun bayyana cewar sojojin kasar suna ci gaba da samun nasara a kan ‘yan ta’addan kungiyar nan da suke kiran kansu gwamnatin Musulunci ta Iraki da Sham (Da’esh ko kuma ISIS) bayan da a yau suka sami nasarar kwato wasu garuruwa na larduna Salahudden da Diyala da suka kasance a hannun ‘yan ta’addan bayan da suka kashe wani adadi mai yawa na su.
Nasarorin da sojojin na Iraki suke ci gaba da samu ya zo ne sakamakon kaddamar da wasu sabbin hare-hare da kasa da sama da sojojin suka yi bugu da kari kan goyon bayan al’umma da suke ci gaba da samu biyo bayan fatawar kaddamar da jihadi a kan ‘yan ta’addan da babban malamin kasar Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya fitar wanda kuma ya sami goyon bayan al’ummar kasar.
1420424

Abubuwan Da Ya Shafa: sistani
captcha