Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, a zaman gaggawa da wakilan kasashen da suke mambobi ne a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C suka gudanar a birnin NewYork na kasar Amurka a jiya Juma’a; Mahalarta zaman taron sun yi Allah wadai da hare-haren ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da kai wa kan fararen hula a yankunan Palasdinawa musamman yankin Zirin Gaza tare da yin kira ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya hanzarta gudanar da zaman gaggawa domin tilastawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila dakatar da wannan ayyukan na ta’addanci kan al’ummar Palasdinu.
Har ila yau mahalarta zaman taron sun tattauna batun ayyukan ta’addanci da nuna wariya na tsawon shekaru kimanin 50 da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta shafe tana gudanarwa a kan al’ummar Palasdinu tare da fayyace hare-haren baya bayan nan da gwamnatin ta haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan yankunan Palasdinawa da cewa; hare-hare ne da suke tabbatar da laifukan yaki a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
A nata bangaren gwamnatin Masar ta gabatar da shawar tsagaita bude wuta, dalilin gabatar da shirin tsagaita wutar shi ne hana H.k. ISra’ila aikew ada sojojin kasa cikin yankin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin Wajen Masar din ya ci gaba da cewa; Masar a shirye ta ke ba zama mai bada lamuni ga dukkanin bangarorin da su ke rikici akan tsagaita wuta sannan kuma da sake bude mashigar da ke tsakanin Gaza da sauran sassan Palasdinu.
1429841