IQNA

Jami'ar Azhar Ta Yi Kira Da A Kafa Wata Cibiyar Kare Kur'ani

20:25 - July 21, 2014
Lambar Labari: 1431850
Bangaren kasa da kasa, babban malamin Jamhuriyar Musulunci ta Iran'ar Azahar ta kasar Masar ya yi kira da akafa wata babbar cibiya ta kasashen musulmi wadda aikinta shi ne kare kur'ani mai tsarki da kuma martabarsa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na A-sharq cewa, Sheikh Ahmad Tayyib babban malamin Jamhuriyar Musulunci ta Iran'ar Azahar ta kasar Masar ya yi kira da akafa wata babbar cibiya ta kasashen musulmi wadda aikinta shi ne kare kur'ani mai tsarki da kuma martabarsa a duniya baki daya, bisa la'akari da cin zarafin da ake yi wa musulmi da kuma wulakanta kur'ani.

A wani rahoton kuma Daliban jami'ar Al'azhar a birnin Alkahira sun gudanar da zanga-zangar Lumana a yau Lititin, rahotani dake fitowa daga birnin Alkahirar masar Sun bayyana cewa a safiyar yau Litinin Jami'an Jamiar Azhar sun gudanar da zanga- zanga domin nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben kasar wanda janar Abdulfatah Sise tsohon ministan tsaron kasar  ya Lashe.
Daliban wadanda suke dauke da fotunan hanbareren shugaban Kasar Muhamad Mursi tare da irin kisan kiyashi da a kayiwa magoya bayansa a masallacin Rabi'atul Adawiya na rare taken yin allawadai ga jami'an tsaron kasar ta Masar.
Har ila yau Daliban sun bukaci Gwamnati da ta sako masu 'yan uwansu dalibai da take tsare da su.
1431096

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha