IQNA

Ayatollah Isa Kasim Ya Soki Kasashen Larabawa Dangane Da Gaza

14:00 - July 28, 2014
Lambar Labari: 1434453
Bangaren kasa da kasa, babbn malamin addini na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya yi kakakusar suka dangane da yadda kasashen larabawa suka nuna halin ko in kula dangane da halin da al'ummar Gaza suke ciki.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Alwasat cewa, Ayatollah Isa Kasim ya yi kakakusar suka dangane da yadda kasashen larabawa suka nuna halin ko in kula dangane da halin da al'ummar Gaza suke ciki sakamakon hare-haren da Isra'ila take kaddamarwa a yankin.

A wani labarin kuma Wata kotu a kasar Bahrain ta yanke hukuncin dauri a gidan kurkuku kan wasu fararen hula sakamakon fafatukar da suke yi na neman gudanar da gyara a harkar siyasar kasar. 
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bada labarin cewa; Wata kotu a kasar Bahrain a yau Laraba ta yanke hukuncin daurin shekaru goma kan mutane 26, yayin da ta daure wasu mutane uku na daban shekaru uku a gidan kurkuku kan zargin hannu a kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda a kasar.
Mutanen 29 sun yi watsi da zargin da jami’an ‘yan sanda ke yi kansu a gaban kotun, amma kotun ta ki saurarensu saboda rahoton da rundunar ‘yan sandan kasar ta gabatar kan su tare da shaidar furucin da ta tatsa daga gare su ta hanyar tursasawa a lokacin da suke tsare a wajen ‘yan sanda.

1433381

Abubuwan Da Ya Shafa: Kasim
captcha