Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, kungiyoyin addini da dama a Najeriya sun yi Allawadai da kisan gllar da sojojin kasar suka yi wa musulmi masu gudanar da zanga-zangar ranar Quds domin nuna goyon baya ga al'ummar palastine a birnin Zaria.
A nasa bangaren Jagoran harkar Musulunci a Nigeriya Sheikh Yakub Ibrahim El-Zakzaki ya bayyana cewar babu wani mutum da ke dauke da makami a lokacin da sojojin gwamnatin Nigeriya sun farma ‘yan uwa da suke gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya, kuma a tsawon tarihin harkar Musulunci a kasar babu wani lokaci da ‘yan uwa suka taba sabar makami domin kare kansu.
A dan takaitacciyar zantawar da ya yi da manema labarai ta hanyar wayar tarho a yau Asabar; Jagoran harkar Musulunci a Nigeriya Sheikh Yakub Ibrahim El-Zakzaki ya bayyana cewa; babu wani dan uwa da ke dauke da makami a lokacin da sojojin gwamnatin Nigeriya suka farma masu a yayin gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a jiya Juma’a, kuma duniya ta isa shaida kan cewa; a tsawon tarihin harkar Musulunci a Nigeriya babu wani lokaci da ‘yan uwa suka taba daukan makami, don haka zamu ci gaba da zaman sauraron irin karyaryakin da zasu dinga furtawa a kanmu.
Sheikh Zakzaki ya kara da cewar yau tsawon shekaru kimanin 40 muna gudanar da irin wannan zanga-zanga, kuma an gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a sassa daban daban na Nigeriya kuma babu abin da ya faru, sai a garin Zariya da sojojin gwamnati suka bude mana wuta ba gaira babu dalili alhali a tsakaninmu akwai mata da kananan yara da kuma tsofaffi.
A jiya Juma’a ce dai sojojin gwamnatin Nigeriya suka bude wuta kan taron jama’a da ke gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a garin Zariya lamarin da ya yi sanadiyar shahadar mutane akalla 31 cikin har da ‘ya’yayen jagoran harkar Musulunci a kasar guda uku Ahmad, Hameed da Mahmud tare da jikkata wasu masu yawa na daban.