Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, World Bulletin cewa mahukunta a kasar Masar sun ce za a bude mashigar Rafah a ranar idi domin bayar da dama ga palastinawa da suka jikka sakamakon hare-haren Isra'ila.
Gwamnatin Masar ta bijiro da shirin tsagaita wuta ga Palasdinawa a Gaza da kuma H.K. Isra’ila. Kakakin ma’aikatar harkokin Wajen Masar BAdar Abdul-Aty ya sanar da cewa; Dalilin gabatar da shirin tsagaita wutar shi ne hana H.k. ISra’ila aikew ada sojojin kasa cikin yankin Gaza.
Kakakin ma’aikatar harkokin Wajen Masar din ya ci gaba da cewa; Masar a shirye ta ke ba zama mai bada lamuni ga dukkanin bangarorin da su ke rikici akan tsagaita wuta sannan kuma da sake bude mashigar da ke tsakanin Gaza da sauran sassan Palasdinu. Abdul-Aty ya kara da cewa a halin da ake ciki a yanzu za su so ganin an kawo karshen hare haren da ake kai wa yankin na Gaza sannan kuma da hana Isra’ila kai wa yankin na Gaza hari ta kasa.
Kawo ya zuwa yanu dai adadin Palasdinawan da su ka yi shahada sun kai daruruwa yayin da wadanda su ka jikkata su ka kai dubbai , sai dai kawo ya zuwa yanzu kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta ce ba ta da labari akan wani shirin tsagaita wuta da gwamnati Masar ta ke magana akan shi.