Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, daya daga cikin sojin yahudawan sahyuniya yana mai alfahari da cewaa cikin rana guda ya kashe kananan yara palastinawa 13 a Gaza bayan day a yi musu kwanton bauna.
A yau ne aka shiga rana ta 28 da Haramtacciyar kasar Isra'ila take kaddamar da hare-haren kiyan kiyashi a kan al'mmar musulmi mazauna yankin Zirin Gaza.
Rahotanni daga yankin Zirin Gaza sun ce a yau jiragen yakin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a kan gidajen jama'a da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya kamar yadda suke yi tun daga farkon yakin, inda suka kashe mutane fiye da 80 tare da jikkata wasu daruruwa, da dama daga cikinsu mata da kanan yara, wanda hakan ya daga adadin wadanda suka yi shahada a cikin makonni 4 a zirin Gaza zuwa mutane dubu daya da dari takwas, wasu fiye da dubu tara kuma sun samu raunuka.
A bangare guda kuma palastinawa 'yan gwagwarmaya sun harba makamai masu linzami fiye da 80 a yau a kan matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida da kuma wasu biranan Isra'ila, amma gwamnatin yahudawa tana ci gaba da boye irin asarorin da take yi, amma rundunar sojin Isra'la ta tabbatar da cewa sojojin yahudawa 64 ne suka halaka a wannan yaki, wasu daruruwa kuma sun samu raunuka.