Shugaban Amurka Donald Trump, tare da wasu shugabannin yankin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza, a yayin wani taro a birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar, a ranar Litinin da ta gabata, a daidai lokacin da ake gudanar da taron, inda ya bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci, tare da barin Masar zuwa birnin Washington bayan sanya hannu kan yarjejeniyar.
Shugaban na Amurka wanda da alama ya ji dadin jagorantar taron, ya yabawa ma'aikatansa da mataimakansa kan cimma yarjejeniyar da ya ce ita ce mafi wahala a cimma.
Trump ya ce "Na yi tunanin cewa watakila wannan zai zama ganawa mafi wahala, kuma watakila ta hanyoyi da dama ya kasance, amma muna da hazaka." "Muna da ƙwazo masu ban mamaki, kuma ƙasashen da ke nan, musamman, sun taimaka mana."
Trump da shugabannin Qatar, Masar da Turkiyya, manyan dillalan yarjejeniyar, sun gudanar da bikin rattaba hannu kan shirin samar da zaman lafiya a Gaza, amma manyan bangarorin biyu da suka kulla yarjejeniyar, wato Isra'ila da Hamas ba su halarta ba.
A Sharm el-Sheikh, shugaban na Amurka ya jaddada yunkurin dakatar da yakin Gaza, yana mai da'awar cewa "ya dauki tsawon shekaru 500 zuwa 3,000 kafin mu kai ga wannan matsayi."
"Za mu rattaba hannu kan wata takarda da ta zayyana dokoki da ka'idoji da wasu batutuwa da dama," in ji Trump a farkon abin da ya bayyana a matsayin taron zaman lafiya a Masar.
"Yana da matukar mahimmanci," in ji shi.
Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas na tafiya "da gaske, da kyau sosai," in ji shi.
"Kowa ya ce ba zai yiwu ba, amma yana faruwa a gaban idanunku," in ji Trump, yana tsaye kusa da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi.
Kashi 80% na tsoffin fursunonin Falasdinu da za a sake su
Yayin da ake sakin fursunonin Palastinawa kusan 2,000 daga gidajen yari na gwamnatin mamaya a yau, domin musayar fursunonin yahudawan sahyoniya 20, wani fitaccen masanin Palasdinawa ya sanar da cewa, 137 daga cikin manyan fursunonin Palastinawa na cikin jerin wadanda za a sako a yau a wani bangare na sabuwar yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin gwagwarmayar Palasdinawa da 'yan mamaya.
Masanin Palasdinawa ya jaddada cewa: Abin da aka cimma nasara ce ga al'ummar Palastinu da tsayin daka.