
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, kakakin dakarun Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas Abu-Ubaida ya bayyana cewa; A shirye suke su koma fagen yaki da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a karshen wa’adin dakatar da bude wuta na tsawon sa’o’i 72 da aka cimma da zai kawo karshe da misalin karfe 8:00 na safiyar yau Juma’a matukar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ki amincewa da sharadin Palasdinawa na kawo karshen killace yankin Zirin Gaza da aka yi tsawon shekaru da hakan ya wurga al’ummar Palasdinu cikin mummunan halin rayuwa.
Abu-Ubaida ya kara da cewa; Sun sanar da tawagar Palasdinawa da ke gudanar da zaman tattaunawa da bangaren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila karkashin sanya idon gwamnatin Masar cewa; kada tawagar ta kuskura ta amince da wata sabuwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta matukar bangaren tawagar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila bai yarda da bukatar daukan matakin kawo karshen killace yankin Zirin Gaza ba.
Kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ta ce ba zata amince ba da jibke dakarun kasa da kasa a yankin zirin Gaza ba. A nasa bangare daya daga cikin shugabanin kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul islami ya ce ba za su amince ba da cewa a jibke dakarun kasa da kasa a zirin Gaza domin yin hakan wani sabon takunkumi ne kuma kare manifofin haramcecciyar kasar Isra’ila ne.
Habib ya ce sharadin da aka gindaya da sake gina zirin Gaza zancen banza ne domin matukar suna raye ba za su amince da ajje makamai ba za su ci gaba da gwagwarmaya har sai sun ’yan yanto kasar Palastinu.
Habib ya ce karamin abida Palastinawa suka bukata wajen dakatar da buda wuta na din din din shine dakatar da hare-haren wuce gona da iri tare da kawo karshen takunkumi na shekaru 8 da Hki take masu.
A gobe juma’a ne wa’adin yarjejjeniyar tsakaita wuta na sa’o’I 72 tsakanin gwagwarmaya da isl’ila zai kawo karshe, amma a kwai yuyuwar sabinta shi domin wani rahoto daga birnin Alkahirar masar yace bangarorin biyu na tattaunawa domin cimma yarjejjeniyar tsakaita na wasu sa’oi 72.
1437987