IQNA

Ana Ajiye Da Kwafin Kur'ani Guda 1100 A Wata Cibiya Da ke Yemen

17:55 - August 20, 2014
Lambar Labari: 1441527
Bangaren kasa da kasa, wata cibiya da ke da babban dakin karatu a birnin San'a na kasar Yemen tana jiye da wasu kwafin al'ur'ani mai tsarki guda 1100 da aka rubuta su da hannu tsawon shekaru ba tare da wata matsala ba.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, yan nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Eram News cewa, yanzu haka wata babbar cibiya da ke da babban dakin karatu a birnin San'a na kasar Yemen tana  jiye da wasu kwafin al'ur'ani mai tsarki guda 1100 da aka rubuta su da hannu tsawon shekaru kuma ana yin amfani das u.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanan dakin karatu na daga cikin manyan wurare da suke ajiye kayan rubuce-rubuce na tarihi wadanda ake adana su domin kiyaye tsari na al'adun mutanen kasar musamman ta fuskar addini da kuma rubutun kur'ani mai tsarki, inda kasar Yemen ta zama daya daga cikin kasashen musulmi da suka shahara a wanann bangare.

Dakin karatun na birnin san'a yana ci gaba da ajiye wasu littafai da aka rubuta a wasu bangarorin na ilimi da suka kai kwafi 3935, kuma dukakninsu an rubuta su ne da hannu wanda maynan malamai shahararru a fagage na ilimi suka rubuta, wanda hakan ya zama abin alfahari ga al'ummar kasar da ma sauran musulmi.

1440967

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha