IQNA

An Kira Ga FIBA Da Ta Janye Dokar Hijabi A Wasan Kwallon Kwado Aurka

20:50 - August 24, 2014
Lambar Labari: 1442673
Bangaren kasa da kasa, an yi kira ga hukumar wasannin kwallon Kwando ta kasar Amurka (FIBA) da ta janye dokar hana saka hijabi da ta kafa ga mata masu wasannin kwallon Kwando a kasar domin hakan shiga hakkin wasu ne.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, daya daga cikin fitattun masu wasan kwallon Kwando a Amurka ta yi kira ga hukumar wasannin kwallon Kwando ta kasar Amurka (FIBA) da ta janye dokar hana saka hijabi da ta kafa ga mata masu wasannin kwallon Kwando a kasar.
A wani labarin kuma Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ta zargi sojojin Amurka da kashe dubban fararen hula a kasar anistan tun bayan kaddamar da hari a kasar tare da mamaye ta a cikin shekara ta dubu biyu da daya zuwa  shekara ta dubu biyu da goma sha hudu da muke ciki.  
A cikin rahoton nata, kungiyar Amnesty International ta tabbatar da cewa akwai dubban fararen hula da ba su da laifin tsaye ba balantana na zaune da sojojin Amurka suka kashe a kasar da suka hada da mata da kananan yara, kungiyar ta ce ta hada rahoton ne bayan samun kwararan dalilai daga mutanen da ta zanta da su a kasar wadanda wasunsu iyalan wadanda aka kashe ne, sai kuma wasu rahotanni na majalisar dinkin duniya dangane da wannan lamari, kuma har yanzu Amurka ba ta biya su diyya ba.
Rahoton na kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ya yi kakkausar suka dangane da tsarin shari'a na kasar Amurka, sakamakon nuna halin ko in kula dangane da ayyukan kisan gilla da sojojin Amurka suke aikatawa kan dubban fararen hula a kasar ba tare da an gurfanar da wadanda suka aikata hakan ba.
1441608

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha