
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Bratha cewa, firayi ministan kasar Itakiya Matio Ranzy ya yaba tare da nuna gamsuwa kan irin matakan babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sistani yake dauka domin fuskantar matsalolin da kasar Iraki take fuskanta a wannan lokaci, musamman batun ayyukan ta’addanci, wanda a kuma a cewa Ayatollah Sistani shi ne bayyana hakikanin koyarwa irin ta addinin muslunci, wato zaman lafiya tare da sauran al’ummomi da kaunar juna.
Babban malamin addinin Musulunci a kasar Iraki Ayatullahi Aliyu Sistani ya shelanta jihadi kan ‘yan ta’adda da nufin kare kasar daga mamayar ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi.
A hudubar sallar juma’arsa ta yau a birnin Karbala na kasar Iraki wakilin babban malamin addinin Musulunci a Iraki Ayatullahi Sistani ya bayyana cewa; Ayatullahi Aliyu Sistani ya bukaci dukkanin al’ummar Iraki da su daura damara tare da sabar makamai domin yakar ‘yan ta’adda da nufin kare kasar Iraki.
Ya kara da cewa; Babban hatsari yana barazana ga kasar Iraki don haka wajibi ne a kan mutanen da suke da damar daukar makami su shiga cikin sahun jami’an tsaron Iraki domin kare kasar, kuma duk wanda ya mutum ya yi shahada a matsayin shahidi.
1442511