Kamfanin dilalncin labaran Iana ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Radad cewa tsohon babban malamin kasar Masar mai bayar da fatawa Shekh Ali Juma'a ya bayyana cewa ya halasta a yi tawassuli da iyalan gidan manzon wato Ahlul bait a shar'ance bisa ga dukkanin hujjoji na addini.
A wani labarin na daban, babban malamin Azhar na kasar Masar ya nuna damuwarsa dangane da samuwar masu akidar kafirta musulmi a wasu kasashen larabawa da na musulmi. Tayyib na jami'ar Al'azhar ta kasar Masar ya bayyana a tashar telbijin ta kasar inda ya bayyana damuwarsa dangane da samuwar akidar kafirta musulmi a wasu kasashen larabawa da na musulmi inda yace masu wannan akida sun eke badda matasa musulmi kuma sun fi makiya musulinci hadari saboda sune suka bayar da fatuwa na kashe Al'ummar musulmi da sunan musulinci kamar yadda yake faruwa a kasashen Siriya,Iraki, Lobnon da kuma abinda yake faruwa yanzu haka a kasar Masar.
Sheikh yace masu irin wannan akida sune suka bada fatawar halarta jinin jami'an 'yan sanda da na Sojoji a kasar ta Masar kuma suke baiwa Al'ummar kasar umarni fito na fito da hukumomi a kasar.
1442924