
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alawatan cewa, cibiyar da ke kula da bayar da fatawar muslunci a kasar Masar ta Darul Ifta ta bayyana abin da 'yan ta'adda a Najeriya na Boko Haram suka suka yi na kafa a bin da suka kira daular musulunci abin bakin ciki ne.
A nata bangaren Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi watsi da ikirarin da shugaban kungiyar Boko Haram Abubkar Shekau ya yi na cewa garin Gwoza da 'yan kungiyar suka kwace daga hannun dakarun Najeriya, a yanzu ba ya karkashin Najeriya, ya koma karkashin daular musulunci.
Abubakar Shekau ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo na mintuna hamsin da biyu da kamfanin dillancin labarai na faransa ya samu, kakakin hedikwatar tsaron, Manjo janar Chris Olukolade ya ce 'yanci da daukacin farfajiyar kasar Najeriya na nan yadda yake.
Kuma ya ce ba za a amince da duk wani ikirari na wata kungiyar ta'adanci dake cewa ta mamaye wani bangare na kasar ba.kuma 'Ba zan iya tabbatar da sahihancin bidiyon ba'
Daga nashi Gwamna jahr Borno Malam Kashin Shetiima a cikin sanarwar da ya fitar ya ce ba zai iya yin tsokaci game da sahihancin bidiyon ba ko kuma akasin haka. Ya ce zai barwa jami'an tsaro su gudanar da bincikensu.
Gwamnan ya ce kuma ba zai iya bayyana irin matakan da hukumomin tsaro suke dauka a Gwoza ba, ko kuma a wani bangare na jahar Borno, amma ya ce yana tabbatarwa da al'ummar jahar Bornon dama sauran jama'a cewa gwamnatin jahar tana baiwa jami'an tsaron da aka tura goyan bayan da suke bukata a kokarin da suke na dakile ayyukan tada kayar baya.
1443741