Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma'a cewa, kwamitin majalisun dokokin kasashen musulmi za ta gudanar da wani zama dangane da palastinu a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan domin tattauna halin da ake ciki bayan kawo karshen yaki a Gaza, da kuma sanin taimakon da al'ummar yankin ke bukata.
A kwanakin baya ma an gudanar da irin wannan taro jamhuriyar muslunci na kungiyar majalisun dokokin kasashen musulmi karkashin kungiyar hada kan kasashen musulmi, taron na kwanaki biyu ya sami halattar shuwagabannin majalisun dokoki na kasashen musulmi talatin, mataimakan shuwagabannin majalisun dokoki goma sha bakawai da kuma wasu kungiyoyin kasa da kasa masu sanya ido a cikin kungiyar guda sha biyar.
Taron dai ya sami halattar shugaban kasar Iran, shugaban majalisar dokokin kasar da kuma alkalin alkalan kasar. A jawabinsa wajen bude taron ya yi kira ga kasashen musulmi su hada kai, su kuma yi amfani da dimbin arzikin da Allah ya basu don samar da wani sauyi babba a duniya, wanda kuma zai bawa musulmi matsayin da ta dace da su a cikinta.
1444802