IQNA

Bahasin Kyawawan Dabi'u Shi Ne kashi 97% Cikin Kur'ani

22:52 - September 05, 2014
Lambar Labari: 1446829
Bangaren kasa da kasa, bahasin kyawawan dabiu shi ne fiye da kashi 97% na dukkanin bahasoshin da aka yia a cikin kur'ani domin kuwa abbabn abin da kur'ani ke koyarwa shi ne shiryarwa zuwa ga kamala wadda kuma ta doru ne kan irin wadannan dabiu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo cewa, tsohon bababn malami addinin muslunci mai bayar da aftawa a kasar Masar Sheikh Ali Jumaa ya bayyana cewa bahasin kyawawan dabiu shi ne fiye da kashi casein cikin dari na dukkanin bahasoshin da aka yia a cikin kur'ani domin kuwa abbabn abin da kur'ani ke koyarwa shi ne shiryarwa zuwa ga kamala wadda kuma ta doru ne kan irin wadannan dabiu wadanda su ne suke misilta addinin muslunci.

Malamin ya ci gaba da bayani yana mai cewa, idana aka kalli akasarin ayoyin kur'ani da suka safka domin tarbiyantar da musulmi da kuma yin aiki mai kyau za mu ga cewa su ne suka fi yawa  acikin kur'ani, wanda kuma hakan shi ne koyar da kyawawan dabiun da kur'ani yake yi wad an adam.

Ya kara da cewa da za a yi amfani da dukaknin koyarawar kur'ani a duniya baki daya, to da an samu zaman lafiya da kwanciyar hakankali domin kuwa kowa zai zama mutumin kirki mai kyakyawar zuciya da kyawawan dabiu, domin kuwa shi kur'ani shi ne hakinnin malami na koyar dad an adam dabiu na gari, shi kuma manzon Allah shi ne malami mai bayani da aikatawa domin koyar da su a aikace.

1445744

Abubuwan Da Ya Shafa: Juma
captcha