IQNA

An Shigar Da Makarantun Kur’ani Cikin Tsarin Makaranru A Mali

7:18 - September 07, 2014
Lambar Labari: 1447328
Bangaren kasa da kasa, an shigar da makarantun kur’ani mai tsarki cikin tsarin makarantu na gwamnati a fadin kasar Mali domin samun dukkanin abubuwan ad suke bukata a bangaren ilimi daga gwamnatin kasar kamar yadda sauran makarantu suke samu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aun Misra Al-Ikhbariyyah cewa an sanar cewa an shigar da makarantun kur’ani mai tsarki cikin tsarin makarantu na gwamnati a fadin kasar Mali domin samun dukkanin abubuwan ad suke bukata a bangaren ilimi daga gwamnatin kasar kamar yadda sauran makarantu suke samu da nufin inganta shi.
Kasar tana daya daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka da ake baiwa makarantun kur’ani mai tsarki matukar muhimmanci, kasanrtuwar akasarin mutanen kasar mabiya addinin musulunci ne da suke kula da lamrin kur’ani, saboda haka wannan shiri na gwamnatin kasar ya samu karbuwa daga al’ummar kasar baki daya.
Yanzu haka dai cibiyoyin da ke kula da makarantun kur’ani na kasar suna cikin shirin fara kididdigar makarantunda kuma sanin adadinsu a fadin kasar, domin mika sakamaon kididdgar ga ma’ikatar kula da addininai, wadda ita ce za ta shiga gaba wajen aiwatar da wannan shiri ta hanayar shugabannin makarantun.
1447093

Abubuwan Da Ya Shafa: mali
captcha