IQNA

Mata Da Ke Sanye Da Hijabi Sun Fi Natsuwa A Kan Wasunsu

22:15 - September 08, 2014
Lambar Labari: 1448187
Bangaren kasa da kasa, wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa mata da suke saka hijabin muslunci sun fi natsuwa a kan wasunsu da ba su saka hijabi a lokacin da sue gudanar da harkokinsu nay au da kullum a tsakanin jama’a.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic News Daily cewa, sakamakon bincike da wasu cibiyoyi a kasar Birtaniya suka gudanar ya tabbatar da cewa mata da suke saka hijabin muslunci sun fi natsuwa da sikka da kansu a fiye da wasunsu da ba su saka hijabi a lokacin da suke gudanar da harkokinsu da mu’amamala.
Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suka gudanar da binciken sun ji ta bakin mata fiye da 600, inda sakamakon binciken nasu ya kai su ga fahimtar cewa akwai wani babban sirri da ke tatatre da saka hijabin musulunci ga mata, duk kuwa da cewa kasar Birtaniya ba kasa ce ta musulmi ba, akasarin mutanen da ke kasar kuma bas u kallon addinin muslunci a matsayin hanya da ta dace da rayuwa, amma duk da irin wannan tasirin matan da suke saka hijabi a kasar sun fi natsuwa.
Wannan bincike dai ba shi ne na farko da aka gudanar ba dangane da matsayin hijabi a tsakanin al’ummar kasar mata da suke saka a tsakanin muslulmi, duk kuda cewa akasarin cibiyoyin da suke gudanar da binciken ba musulmi ba ne, amma dai wannan shi ne irin sakamakon da suke fitarwa  akowane lokaci.
1447478

Abubuwan Da Ya Shafa: briton
captcha