Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Yaum Sabi cewa, a zantawar da ta hada babban malamin jami’ar Azahar Ahmad Tayyib da kuma ministan harkokin wajen Saudiyyah Saud Faisal, malamin ya bayyana cewa masu akidar takfiriyya suna aiki ne domin bata sunan addinin Musulunci da kuma rusa tafarkin gwagwarmaya.
Ya ci gaba da cewa a cikin watannin bayan nan ayyukan da masu akidar takfiriyyah su ka yi ya tabbatar da cewa ba su da wata alaka da addinin Musulunci, kuma kiyayyarsu da sukkanin musulmi ne baki daya. Malamin ya kuma kirayi dukkanin al’ummar musulmi da su hada kawukansu a wuri guda domin kalubalantar makiyan addinin Musulunci.
1448249