IQNA

Nasarar Juyin Islama A Iran Na Da Aalaka Da Wasu Ayoyin Kur'ani

21:48 - September 11, 2014
Lambar Labari: 1449080
Bangaren kasa da kasa, shugaban gidan radiyon kur'ani a birnin Tuni na kasar Tunisia Sa'id Alajaziri ya gayyaci shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Iran a Tunisia zuwa dakin watsa shirinsu domin ganin abin da ake gudanarwa.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, a lokacin da shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Iran a Tunisia Sadiq Ramezani ya isa bababn dakin watsa shirye-shirye na wannan radio, ya gana da manyan jami'an wurin da suka hada das hi kansa bababn daraktan radiyon Sa'id Aljaziri, inda ya bayyana cewa ko shakka babu gidan radiyon ya yi tasiri matuka musamamn ma ganin cewa an kafa shi ne bayan motsin da aka samu a kasashen larabawa.

Ya ci gaba da cewa kasar Iran tana babban tasiri a cikin a cikin fadakar al'ummomin larabawa da na musulmi, domin kuwa juyin juya halin muslunci da aka yi a kasar karakshin jagorancin marigayi Imam Khomenei shi ne babban dalilin fadakar da aka samu tsakanin al'ummomin musulmi da na larabawa a cikin wadannan yan shekaru, kuma tasirin hakan ne ya kai ga kifar da gwamnatoci da suke da alaka da yahudawa.

A nasa bangaren shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Iran akasar ta Tunisa Sadiq Ramezani ya bayyana cewa za su ci gaba da kara fadada alaka ta 'yan uwantaka tsakaninsu da 'yan uwansu an Tunisia, tare da bayar da dukaknin gudunmwa domin kara fadada ayyukan kur'ani da kuma koyar da mutane hakikanin abin da wannan littafi mai tsarki ya kunsa.

Daga karshe ya mika kyautar kwafin kur'ani mai tsarki da aka wallafa a kasar Iran ga wannan gidan radio da ke watsa shirye-shirye na kur'ani mai tsarki a kasar ta Tunisia.

1448638

Abubuwan Da Ya Shafa: tunis
captcha