IQNA

AnGabatar Da Shawar Horar Da Daliban Kur'ani Fiye Da 10,000 A Malayzia

22:20 - September 13, 2014
Lambar Labari: 1449612
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar harkokin ilimi ta kasar Malayzia ta gabatar da wata shawara ga bangarorin da ke kula da harkokin ilimi kur'an da kuma makarantunsu a cikin kasar Malayzia kan horar da wasu dalibai kim anin 10,920 a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jadid Alyaum cewa, ma'aikatar ilimi ta kasar Malayzia ta gabatar da shawara ga bangarorin malamai da ke kula da harkokin ilimin kur'an da kuma makarantunsu a cikin kasar Malayzia kan horar da wasu daga cikin dalibai kimanin 10,920 a kasar baki daya.
Wannan shiri dai yana nufin samar da gogaggun makaranta da mahardata ne da za su samu kyakkayawan horo, wanda zai ba su damar iya koyar da wasu ta hanyoyi na zamani mafi sauki wajen fahimta, domin su zama za su iya gogawa da takwarorinsu an kasashen musulmi da ma duniya baki daya.
Kasar Malayzia dai na daga cikin kasashen musulmi da suke bayar da muhimmanci matuka ga harkoki na karatu da harder kur'ani mai tsarki, inda akan shirya gasa ta duniya a kasar tun kimanin shekaru fiye da hamsin da suka gabata, inda kasashen musulmi da na larabawa suke halarta.
1449237

Abubuwan Da Ya Shafa: Malayzi
captcha