IQNA

Kokarin Cibiyar Fatawa Ta Masar Na Yada Fahimtar Addini A Afirka

22:03 - September 15, 2014
Lambar Labari: 1450411
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar da ke kula da harkokin addini da kuma bayar da fatawa a kasar Masar ta fara aiwatar da wani shiri na wayar da kan al'ummomin kasashen yammacin nahiyar Afirka kan sahihiyar fahimta ta addini.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, a cikin wannan makon ne cibiyar da ke kula da harkokin addini da kuma bayar da fatawa a kasar Masar ta fara aiwatar da wani shiri na wayar da kan al'ummomin kasashen yammacin nahiyar Afirka kan sahihiyar fahimta ta addinin musulunci, maimaikon rungumar tunani maras tushe da sunan addini.

Bayanin ya ci gaba da cewa tawagar cibiyar ta ziyarci birnin Kaduna na tarayyar Najeriya, inda ta gana da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar da suka hada da ministan harkokin wajen kasar gami da babban jami'I mai bayar da shawara kan harkokin addinai ga shugaban kasar, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi addini da kuma yadda za a taimaka wajen dakile yaduwar tsatsauran ra'ayi da ta'addanci.

Tawagar ta gudanar da wani zama tare da daruruwan musulmi a wani masallaci da ke birnin Kaduna, inda aka gabatar da jawabai da kuma fadakarwa kan wajabcin bayyana addinin muslunci ta hakikianin surarsa ta zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai, maimakon dakar munanan akidu masu bata sunan muslunci a ianun wadanda ba musulmi ba.

1449549

Abubuwan Da Ya Shafa: Ifta
captcha