IQNA

Babban Mai bayar Da Fatawa A Palastinu Ya ce ISIS Ba Musulunci Suke Yi Ba

22:06 - September 15, 2014
Lambar Labari: 1450412
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a palastinu baki daya Sheikh Muhammad Hussain ya bayyana cewa kungiyar da ake kira Daular Musulunci a Iraki da Sham gungu ne na 'yan ta'adda tantagarya.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na na jaridar Ukaz ta Saudiyya cewa, Sheikh Muhammad Hussain a cikin wani bayani da ofishin da ke a cibiyar fatawa  a Qods ya ce 'yan ta'addan kungiyar ISIS bai halasta ba a shar'ance a danganta su da addinin musulunci, domin dukkanin abin da suke yin a ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen siriya da Iraki ya yi hannun riga da addinin muslunci da kuma koyarwar sunna irin ta manzon Allah.
Shehin malamin ya yi Allawadai da rusa kabrukan annabawa da salihan bayi gami da masallatai da majami'oi da 'yan kungiyar ta ISIS suke yi yanzu ahak a cikin kasashen Syria da Iraki, tare da muzantawa da kuma cin zarafin marassa rinjaye da suka mamaye yankunansu, musamman kiristoci da kuma Izidawa da kuma sauran bangarori na musulmi sunna da shi'a.
Mataimakin ministan harkokin wajen jamhuriyar muslunci a nasa bangare ya bayyana ‘yan ta’adda na kungiyar ISIS da ke kai hare-hare a cikin kasashen Iraki da Syria da cewa suna aiwatar da wani shiri ne da makiya musulunci suka shirya.
Ya kara da cewa, kungiyar ‘yan ta’addan ta yi ikirarin cewa tana kai hare-hare ne a cikin siriya da Iraki domin kare sunnah, duk kuwa da cewa akasarin mutanen da ta kashe a wadannan kasashen ‘yan Sunnah ne, a lokaci guda kuma kungiyar ta ki ta yi ko da Allawadai ne da kisan gillar da Isra’ila ke yi wa musulmi ‘yan sunnah a zirin gaza, lamarin da ya kara fito da irin alakar da ke tsakaninta da Isra’ila a fili.
1449696

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha