IQNA

Azahar Ta Zama Ta Salafawa Bayan Nuna Fushi Da Ziyarar Ahmad Kirmah A Qom

19:26 - September 17, 2014
Lambar Labari: 1451244
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar ilimin addinin muslunci ta kasar Masar wato cibiyar Azhar ta zama karkashin tasirin salafawa inda ta fito karara ta nuna fushi da kuma damuwa dangane da ziyarar da daya daa cikin malamanta ya kai birnin Qom.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisriyun cewa, cibiyar ilimin addinin muslunci a kasar Masar ta Azhar ta fito karara ta nuna fushi da kuma damuwa dangane da ziyarar da sheikh Ahmad Karima daya daa cikin malamanta a bangaren shari'a ya kai birnin Qom cibiyar ilimi a jamhuriyar musulunci ta Iran.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mataki ya zo ne bayan da shehin malamin ya jagoranci wata tawaga ta dalibai da kuma masu binciken ilimin addini suka zo Iran domin ganawa da malaman mazhabar Ahlul bait a bababr cibiyar ilimi ta kasar da ke birnin Qom, inda ya samu tabe daga malamai tare da bashi kyautukan littafai domin samin damar kusanto da fahimta  atsakanin mabiya mazhabobin addinin muslunci, lamarin da cibiyar Azhar ta kalle shi ta wata mahanga ta daban.

Yanzu haka dai malamin ya gurfana a gaban kwamitin bincike na cibiyar, wanda hakan zai iya zama sanadiyyar rasa aikinsa na babban malamin oyar ilmomin shari'a a wannan jami'a, wanda kuma hakan ya sanya masana kan harkokin cibiyar yin tunanin cewa baya rasa nasaba da tasirin wahabiyanci da aka fara samu a wannan cibiya, wanda zai bar mummunan tasiri ga ayyukanta.

1450681

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha