Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Saumariyyah News cewa, a zaman da ya gudanar jiya babban kwamitin manyan malaman jami’ar Azahar ta kasar Masar ya bayyana abin da ake kira daular musulunci ta gungun ‘yan ta’addan IS da cewa bau abin da ya hada hakan da addini.
Bayanin ya ci gada cewa tun kafin lokacin wadannan gungun ‘yan ta’adda da suka fito daga kasashe da dama da suke dauke da wata mummunar akida da tunani maras kan gado, sun hadu ne domin yin abin da suke kira jihadi amma akan musulmi da kabrukan bayin Allah, wanda hakan bas hi da wata alaka da koyarwar musulunci balantana sunnar manzo, tare da bayyana hakan a matsayin balai mafi girma da al’ummar musulmi ke fuskanta a halin yanzu.
Yun bayan kafa kungiyar ‘yan ta’addan ISIS a kasdar Iraki wadda ta rikide daga kungiyar alkaida a Iraki ta koma abin da ake kira daular musulunci a Iraki da sham, kungiyar ta aikata ayyukan ta’addanci da dama akan al’ummar kasar Iraki, da hakan ya hada tayar da bama-bamai da kuma kai hare-hare kan jami’an da fararen hula da wuraren ibada na mabiya mazhabobi da addinai a kasar, kafin daga baya tare da taimakon wasu kasashen yankin suka kwace iko da wasu yankuna a Syria da Iraki, inda suka koma suna kiran kansu daular musulunci.
1452380