IQNA

Amurka Ba Ta Da Hurumin Yaki Da 'Yan Ta'addan IS

17:00 - September 25, 2014
Lambar Labari: 1453922
Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya jaddada cewar kasar Amurka bat a hurumin yaki da IS domin it ace ta kirkiro su domin bata sunan addini muslunci.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, Sayyid Nasrullah ya bayyana hakan a jawabin day a gabatar wanda ta shar talabijin ta almanar ta watsa, ya ci gaba da cewa Siriya ita ce kashin bayan gwagwarmaya don haka 'yan gwagwarmaya ba zasu taba zuba ido suna ganin ana neman karya kashin bayansu ba.
A jawabinsa kan bikin tunawa da zagayowar ranar 'yantar da yankin kudancin Lanabon daga mamayar yahudawan sahayoniyya karo na 13 a yammacin yau Asabar: Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar hakika al'ummar yankin gabas ta tsakiya zasu afka cikin kangi mai tsananin duhu da tarko da babu mafita daga gare shi matukar kasar Siriya ta fada karkashin ikon kasar Amurka. Kamar yadda dukkanin musulmi da kiristoci suke fuskantar babban hatsari daga 'yan tawayen da suke yaki a kasar Siriya masu dauke da akidar kafirta musulmi tare da samun tallafi daga kasar Amurka da kawayenta na yammacin Turai gami da 'yan koranta na kasashen larabawa da na yankin.
Nasrullahi ya fayyace cewar yakin kasar Siriya tamkar yakin duniya ne aka fara sakamakon daukin da kasashen duniya suke kai wa ga 'yan ta'adda a kasar, don haka kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi ta dauki matakin tallafawa gwamnatin Siriya da take matsayin kashin bayan gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya.
Har ila yau babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya fayyace irin gagarumar rawar da kungiyarsa ta taka domin ganin an warware rikicin Siriya da hanyar lumana, amma 'yan tawayen kasar suka ki amincewa sakamakon goyon bayan da suke samu daga manyan kasashen yammacin Turai da wasu gwamnatocin kasashen larabawa da suka mika kai ga bakar siyasar Amurka da h.k.Isra'ila.
1453351
 

Abubuwan Da Ya Shafa: Nasrullah
captcha