
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albawabah cewa, yanzu haka an tarjama littafin nan mai suna muslunci da yammacin duniya da kuma takura yancin gudanar da addinai wato «Islam and the West: The Limits of Freedom of Religion» a cikin harshen turancin ingilishi domin amfanin masana wannan harshe a cikin kasashn turan da kuma sauran kasashen duniya.
Wannan littafi dai ya yi dubi ne dangan eda rayuwar musulmi mazauna kasashen yammacin turai da kuma irin kalu bale da suke fuskanta a cikin irin wadannan kasashe wadanda ban a musulmi ba ne, kuma 'yan asalin wadannan kasashe su am ba musulmi ba ne, duk kuwa da cewa musulmi sukan samu damar gudanar da ayyukansu na ibada a wasu kasashen a cikin 'yanci gwargwado, amma a wasu kasashen abbu haka, domin kuwa gwamnatoci sun bayar da damar hakan, wasu amsu kyamar musulmi suna takura ma mabiya muslunci a duk inda suka gansua acikin kasashensu.
Abubuwan da suka farua a cikin wasu kasashen turana cikin yan lokutan na sun isa su zama a bin buga misali, domin kuwa an samu wadanda suka shirya fina-finai da ma yin rubutu na batunci ga addinin muslunci da nufin tsokana ga musulmi na kasashensu da kuma na duniya baki daya, amma duk da haka kuma gwamnatocin wadannan kasashe suna kallon haka a matsayin 'yancin albarkacin bayyana ra'ayi.