IQNA

Shugaban Majami'ar Vatican Ya yi Kakkausar Kan 'Yan ta'adda A Syria Da Iraki

23:03 - October 04, 2014
Lambar Labari: 1457127
Bangaren kasa da aksa, a wani zama da manyan limaman fadar Vatican suka gudanar sun jaddada rashin amincewarsu da abin da 'yan ta'addan ISIS suke yia cikin kasashen Iraki da Syria da sunan addinin muslunci.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, a jiya a zama da manyan limaman fadar Vatican suka gudanar sun jaddada rashin amincewarsu da abin da 'yan ta'addan ISIS suke yia  cikin kasashen Iraki da Syria wanda bayyana hakinain tunaninsu na dabbanci dangane da bila adama, inda suke kashe musulmi da kirista ba tare da wani banbanci ba.

A nasa bangare kuwa shugaban kwamitin siyasar harkokin waje da tsaro a majalisar dokokin jamhuriyar muslunci  ala'uddin  ya sheda cewa, hare-haren Amurka kan 'yan ta'addan ISIS a arewacin Iraki burga ce kawai.  
Ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada shi da tashar talabijin ta Al-alam, inda ya ce Amurka ce tare da wasu kawayenta suka kafa kungiyar 'yan ta'addan ISIS da ke kai hare-hare a cikin kasashen Iraki, Syria da kuma labanon, suna kashe musulmi da wanda ba musulmi duk da sunan jihadi, domin kawai a bakanta fuskar addinin muslunci a idon duniya.
Ya kara da cewa Amurka ta yi niyyar ta dauke hankulan al'ummomin duniya ne daga irin tabargazar da yadawan sahyuniya suke aikatawa, amma tuni al'ummomin duniya sun riga sun fadaka, kuma duniya ta fahinci cewa yahudawan sun sha kashi a yakin sun a baya-bayanan,  domin kuwa an kashe mata sojoji da dama, kuma ba ta cimma ko daya daga cikin dalilan da ta ce tana yin yakin saboda su ba, abin da ta iya yi shi ne kawai kashe mata da kananan yara da rusa makarantu da masallatai da asibitoti.

1456537

Abubuwan Da Ya Shafa: pop
captcha