Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa a zantawar da ta hada shi da shekh Zafir Najjar shugaban majalisar malaman addinin musulunci a kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa babbar manufar kasashen turai ta kafa kungiyar 'yan ta'addan Daesh ita ce kawar da hankulan al'ummomin duniya baki daya daga barnar da Isra'ila take tafkawa a kan al'ummomin palastinu.
A nasa bangaren a jawabinsa a yayin bude zaman Majalisar Shawarar ta Musulunci a jiya Laraba, ya fayyace cewa yau fiye da shekaru uku ke nan gwamnatin Amurka da wasu kawayenta suna taimaka wa ayyukan ta’addanci a kasar Siriya. Sannan wasu daga cikin kasashen da suka shiga cikin sahun kawancen Amurka kan yaki da ta’addanci, suna daga cikin kasashe masu goyon bayan ayyukan ta’addanci a kasar ta Siriya, kuma mafi yawan ‘yan ta’addan kasa da kasa ta cikin kasashensu suka tsallaka zuwa cikin kasar Siriya.
Ya kara da cewa shin gwamnatin Amurka tana zaton wani zai gaskata da’awarta ta yaki da ta’addanci ne, alhali har yanzu tana kan bakanta na ci gaba da taimaka wa ayyukan ta’addanci, inda ko a cikin makon da ya gabata sai da ta sake gabatarwa Majalisar Dokokin kasar ta Amurka bukatar ci gaba da tallafawa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya.
A cikin wanann makon ne dai mataimakin shugaban Amurka ya fito ya ambaci sunayen kasashen da suke daukar nauyin ayyukan ta'addanci na kungiyar ta Daesh da suna yunkurin kifar da gwamnatin Syria, lamarin da bai yi nasara ba.
1455934