Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa, a karon farko an fara gudanar da gasar tajwidin kur’ani mai tsarki a birnin Nuwakshout na Mauritaniya tare da halartar makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki daga sassan kasar ta Maurtaniya.
Babban daraktan cibiyar kula da harkokin kur’ani a kasar mauritaniya Khalid Garib ya bayyana cewa, an saka ma wannan gasa suna Mizmar Al-zahbi, kuma babbar anufar fara gudanar da irin wannan gasa wanda shi ne farko a kasar Mauritaniya, it ace karfafa gwiwar makaranta na kasar da su shiga cikin dukkanin harkoki na kur’ani baki daya a matsayi na kasa da kasa, da hakan ya hada har da gasar tajwidi da ake gudanarwa a duniya, ba sai karatu ko harda ba.
A nasa bangaren shugaban kafofin yada labarai na kasar Mauritaniya Ali Sheikh Bilmalih ya bayyana cewa, suna da shirin bayar da kyuatuka ga wadanda suna kwazo na kudade da kuma wasu kyautuka wadanda ban a kudi, haka nan kuma za su kai wasu daga cikin wadanda suka nuna kwazo zuwa kasar Masar domin shakatawa.
1458794