IQNA

Taron Idil Gadir A Karon farko A Babban Birnin Yemen

21:43 - October 13, 2014
Lambar Labari: 1459787
Bangaren kasa da kasa, a karon farko an gudanar da tarukan idi na Gadir a birnin sana’a fadar mulkin kasar Yemen tare da halartar dubban daruruwan mutane mabiya mazhabar iyalan gidan manzo.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Eram cewa, a jiya a karon farko an gudanar da tarukan idi na Gadir a birnin sana’a fadar mulkin kasar Yemen tare da halartar dubban daruruwan mutane magoya bayan kungiyar Ansarullah kuma mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne taron Gadir wanda mabiya tafarkin ahlul bait suka shirya a birnin na San’a wanda kuma ya isar da sako ga dukkanin al’ummar kasar kan cewa mabiya tafarkin iyalan gidan amnzo masu son zaman lafiya ne tare da dukkanin bangarorin kasar, wadanda suke bin mazhabobi na addini daban-daban, tare da kiran kowa duk mai bukata da ya halarci tarukan ba tare da wata tsangwama ba.

Jagoran mabiya tafarkin iyala gidan manzo na Ansarllah Abdulmalik Huthi shi ne ya jagoranci gudanar da tarukan, a ha;lin yanzu dai mabiya tafarkin iyalan gidan manzo ne suke rike da komai ta fuskar gudanarwa a kasar, inda kuma suka ki amincewa da duk wani mataki wanda zai kawo rarraba  atsakanin al’ummar kasar ta Yemen.

Gudanar da wannan babban taro mai albarka na dauke da sakonni da ke nuni da cewa hasken kira na iyalan gidan manzo yana ci gaba da kara shiga dukkanin lunguna  acikin nasara akasar ta Yemen.

1459513

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha