IQNA

Darussan Musulunci A Cikin Harsunan Duniya A Masallacin Azhar

21:50 - October 13, 2014
Lambar Labari: 1459788
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da wani shiri na bayar da horo kan addinin muslunci a cikin harsuna daban-daban na duniya a babban masallacin jami’ar Azahar da ke birnin Alkahira na kasar Masar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum sabi cewa, a cikin wannan makon ne aka fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan addinin muslunci a cikin harsuna na duniya a babban masallacin jami’ar Azahar.

Wannan shiri dais hi ne irinsa na farko da aka fara gudanarwa da nufin kara ilmantar da mabiya addinin muslunci da suke kai ziyara a kasar Masar da suke da sha’awar sanin imlmomi na addini a bangarori daban-daban, kuma hakan ya hada musulmi ne wadanda ba larabawa ba, domin kuwa shirin ya kebanci ‘yan kasashen ketare ne kawai wadanda ba su Magana da harshen larabci.

Sheikh Husamuddin Alazhari daya ne daga cikin masu koyar da fikihu a jami’ar Azhar ya bayyana cewa, daga cikin wadanda suke amfana da shirin akwai wadanda sun musulunta ne daga kasashen yammacin turai, inda ake koyar da su wasu daga cikin ilmomin kur’ani mai tsarki, da kuma fikihun shari’ar musulunci gami da wasu ilmomin na daban da suka hada har harshen larabci, wanda kuma hakan yana da babban tasiri ga mutane, musamman ma ganin cewa shiri na dan lokaci ne wanda kuma zai amfanar matuka kamar dai yadda da dama daga cikin mahalartan suka bayyana.

1459404

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha