IQNA

Yaki Da 'Yan Takiriyyah Shi Ne Hizbullah Ta Sanya A Gaba

22:59 - October 14, 2014
Lambar Labari: 1460259
Bangaren kasa da kasa, Jagoran kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya ziyarci yankin Bika da ke gabacin kasar Lebanon a kan iyakokin kasar da Syria.

A yayin da yake ganawa da wasu manyan kwamandoji da kuma mayaka na kungiyar ta Hizbullah da ke yankin, Sayyid Hassan Nasrullah ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya a yakin da suke yi a kan makiya, inda ya ce ‘yan ta’addan Takfiriyya ba za su yi nasara a kan gwagwarmayar da aka kafa ta a kan tawakkali ga Allah ba.

Wannan ziyara ta Sayyid Nasrullah a yankin Bika dai ta zo ne a lokacin da ‘yan ta’addan Takfiriyya ke kokarin samun damar wucewa da kayayyakin bukatarsu daga Lebanon zuwa yankin Kalamun na kasar Syria da ke kusa da iyakar kasar da Lebanon, wanda mayakan Hizbullah suka kori ‘yan ta’adda daga cikinsa a lokutan baya.

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya jaddada cewar kasar Siriya ita ce kashin bayan gwagwarmaya don haka 'yan gwagwarmaya ba zasu taba zuba ido suna ganin ana neman karya kashin bayansu ba.
Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar hakika al'ummar yankin gabas ta tsakiya zasu afka cikin kangi mai tsananin duhu da tarko da babu mafita daga gare shi matukar kasar Siriya ta fada karkashin ikon kasar Amurka.
Kamar yadda dukkanin musulmi da kiristoci suke fuskantar babban hatsari daga 'yan tawayen da suke yaki a kasar Siriya masu dauke da akidar kafirta musulmi tare da samun tallafi daga kasar Amurka da kawayenta na yammacin Turai gami da 'yan koranta na kasashen larabawa da na yankin.
Nasrullahi ya fayyace cewar yakin kasar Siriya tamkar yakin duniya ne aka fara sakamakon daukin da kasashen duniya suke kai wa ga 'yan ta'adda a kasar, don haka kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi ta dauki matakin tallafawa gwamnatin Siriya da take matsayin kashin bayan gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya.
Har ila yau babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya fayyace irin gagarumar rawar da kungiyarsa ta taka domin ganin an warware rikicin Siriya da hanyar lumana, amma 'yan tawayen kasar suka ki amincewa sakamakon goyon bayan da suke samu daga manyan kasashen yammacin Turai da wasu gwamnatocin kasashen larabawa da suka mika kai ga bakar siyasar Amurka da h.k.Isra'ila.
1460026

Abubuwan Da Ya Shafa: hizbullah
captcha