IQNA

Cibiyar Bayar Da Fatawa A masar Ta Yi Allawadai Da Cin Zarafin Musulunci A Amurka

23:10 - October 14, 2014
Lambar Labari: 1460260
Bangaren kasa da kasa, bababr cibiyar da k kula da ayukan fatawa a kasar ta yi kakausar suka da kuma yin Allah wadai dangane da yadda wani dan jarida na Amurka ya ci mutuncin muslunci.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na Alwafd cewa, mataimakin shugaban babbar cibiyar ayukan fatawar muslunci a kasar Ibrahim Najam ya yi kakausar suka da kuma yin Allah wadai dangane da yadda wani dan jarida na Amurka ya ci mutuncin muslunci ta hanayar kafofin yada labarai.

A lokacin da yake gabatar da wani shiri na talabijin Nabil Mahir dan kasar Amurka ya rika yi yana izgili ga addinin muslunci, tare da bayyana cewa akasarin mabiya addinin muslunci suna bin akida irin ta 'yan ta'adda ne, domin kuwa  acewarsa haka addini yake koyar da mabiyansa, kuma a cewarsa musulmi suna goyon bayan ayyuakn da 'yan akaida da sauransu suke aikatawa da sunan muslunci.

Malam Ibrahim Najam ya ce koshakka babu ba su goyon bayan wuce gonad a iri a cikin addini ko aikata munan ayyuka na ta'addanci da sunan muslunci, amma kuma hakan bay a nufin cewa kowa zai ci zarafin addini saboda abin da wasu 'yan tsiraru suke aikatawa da sunan wannan addini, domin kuwa abin da suke yi ba su wakiltar muslunci, haka nan kuma ba su wakiltar al'ummar musulmi.



1460074

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha