IQNA

‘Yan ta’addan Daesh Sun Yi Barazanar Daga Tutarsu A kan Fadar Vatican

22:03 - October 15, 2014
Lambar Labari: 1460702
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ‘yan ta’addan daesh da aka fi sani da ISIS ta yi barazanar kaddamar da hare-hare kan fadar Vatican tare da mamaye da kuma kwace iko da ita da kuma dora tutar kungiyar a kan fadar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga tashar talabijin ta Al-alam cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’addan daesh da aka fi sani da ISIS ta yi barazanar kaddamar da hare-hare kan fadar Vatican tare da mamaye da kuma kwace iko da ita da kuma dora tutar kungiyar a kan fadar ta Vatican.

A wani labarin kuma jaridar times da ake bugawa a kasar birtaniya ta bayar da wani rahoto da ke cewa 'yan ta'addan ISIS suna sayar da mata da kananan yara da suke kamewa suna yin garkuwa da su a Syria da Iraki.

Jaridar ta ce 'yan ta'addan na ISIS sun bude kasuwar sayar da mata da kananan yara a Mausil da ke cikin Iraki da kuma Riqqah da ke cikin Syria, yayin da wasu jaridun kasashen larabawa suka bayar da wasu rahotannin da ke cewa 'yan ta'addan na ISIS suna sayar da mata ne bayan sun gama yi musu fyade, kuma ana shigar da su cikin kasashen Saudiyya da Jordan bayan an sayar da su.

Wasu rahotannin kuma sun tabbatar da cewa 'yan ta'addan na ISIS suna sayar da kananan yara da suke sacewa a Syria da Iraki ga haramtacciyar kasar Isra'ila, inda a kan shigar da su cikin kasar Turkiya tare da hadin baki da wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar, daga nan kuma za a dauke su a cikin jirgi zuwa birnin Tel aviv na haramtacciyar kasar israila.

1460593

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha