IQNA

Sojojin Yahudawan Isra'ila Na Ci Gaba Da Takura ma Musulmi A Qods

22:24 - October 18, 2014
Lambar Labari: 1461401
Bangaren kasa da kasa, sojojin yahudawan Isra'ila suna ci gaba da daukar matakai na takura ma musulmi mazauna birnin Qods dangan eda yadda suke gudanar da harkokinsu na ibada a cikin masallaci mai alfarma


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Worl Bulletin cewa, a cikin kawanakin nan sojojin yahudawan Isra'ila suna ci gaba da daukar matakai na takura ma musulmi mazauna birnin Qods dangane da yadda suke gudanar da harkokinsu na ibada a cikin masallaci mai alfarma wanda ke da matsayi na musamman a wajen al'ummar musulmi.



Wata kungiyar yahudawa mai fafutukar kare hakkin bil adama a HKI, ta fitar da wani rahoto da ke cewa yahudawa mahukuntan birnin Qods na shirin rushe dukkanin gidajen palastinawa da ke yankin Hayyul Bustan a gabacin birnin.



Rahoton kungiyar ya ci gaba da cewa mahukuntan birnin Qods suna son su rushe dukkanin gidajen palastinawa da ke yankin Hayyul Bustan ne bisa hujjar cewa an gina gidajenne ba bisa ka'ida ba, a maimakon haka za su mayar da wuri wani katafaren wurin shakatawar yahudawa, kuma za a bai wa yahudawa damar yin gine-gine a gefen wurin, tatre da haramtawa duk wani bapalastine zama a yankin baki daya.



Wannan rahoton kungiyar yahudawan mai fafutukar kare hakkin bil adama ya ce, babu kamshin gaskiya a cikin abin da gwamnatin Isra'ila ke rayawa, kan cewa palastinawa sun gina gidajen nasu ba bisa ka'ida ba, wannan duk yana cikin shirin mayar da birnin Qods da kewaye mallakin yahudawa ne kadai, wanda gwamnatin Natanyaho ke hankoron aiwatarwa.



1461051

Abubuwan Da Ya Shafa: yahudu
captcha