IQNA

Danfin wasu ‘yan birtaniya Da suka Shiga Daesh Sun Jaddada Hadin kai A Tsakanin Musulmi

23:19 - October 19, 2014
Lambar Labari: 1461867
Bangaren kasa da kasa, dagin wasu daga cikin matasan kasar Birtaniya mabiya addinin musulunci da suka shiga cikin kungiyar nan ta ‘yan ta’adda Daesh ko kuma ISIS kamar yadda aka fi saninta sun jaddada cewa abin da dangin nasu suka yi ba zai raba kan al’ummar musulmi na kasar Birtaniya ba kuma ana yi musu fatan su su shiriya su tuba.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, a jiya dagin wasu daga cikin matasan kasar Birtaniya mabiya addinin musulunci da suka shiga cikin kungiyar nan ta ‘yan ta’adda Daesh ko kuma ISIS kamar yadda aka fi sanint, wadanda suka tafi kasashen Syria da Iraki suna kashe musulmi da sunan jihadi a addinin muslunci, dangin nasu sun jaddada cewa abin da yan uwansu suka yi ba zai raba kan al’ummar musulmi na kasar Birtaniya ba kuma ana yi musu fatan su su shiriya su tuba su bar wannan kungiya ta ta’addanci da ke bata sunan addinin muslunci da musulmi a duniya.

Baynain ya ci gaba da cewa kasar Birtaniya dai it ace kasa ta farko a nahiyar turai da take da yawan ‘yan ta’adda da suka shiga wannan kungiya da ke kashe musulmi tana bata sunan addinin muslunci, bayan samun horo a hannun wasu malaman wahabiyawa da ke gurbata tunanin matasa daga cikin musulmin kasashen turai da kuma na larabawa, wadanda wasu daga cikin gwamnatocin larabawa musamamn ma Saudiyya suke daukar nauyin hakan.

‘Yan ta’addan dai sun shelanta yaki ne kan kasashen musilmi, tare da kafirta duk wani wanda bai shiga cikinsu ba, ko da kuwa shi ma yana dauke da wannan akida ta wahabiyanci da kafirta musulmi.

1461202

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha