Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa taron da ke gudana na malaman musulunci da ke goyon bayan gwagwarmaya da zaluncin yammacin turai da yahudawan sahyuniya a birnin Beirut an jaddada wajabcin ajiye batun mazhaba a cikin batun gwagwarmaya ta gaskiya.
A lokacin bayaninsa mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Na’im Qasim ya bayyana cewar irin kwarewar da kungiyar Hizbullah ta samu ta sanya ta zama abar koyi a fagen yaki da jihadi haka nan kuma a fagen zaman lafiya da aiki tare da abokan zama da tarayya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a yau din nan Juma’a, inda yayin da yake magana dangane da ayyukan ta’addancin da ‘yan kungiyar Da’esh (ISIS) da Jabhatun Nusra (Al-Nusra Front) suke aikatawa a kasashen Siriya da Iraki da kuma kokarin da suke yi na shigowa cikin kasar Labanon ya bayyana cewar: Mu dai ba ma jin tsoron wannan ihu bayan harin da ake ta yi da sunan Da’esh ko al-Nusra da dukkanin makamantansu”. Sheikh Qasim ya ci gaba da cewa: Wadannan kungiyoyi dai ba sa wakiltan Musulunci, daga kusa ne ko kuma daga nesa. A fili yake cewa wadannan mutanen babu wani abin da ya hada su da wannan addini na Ubangiji.
Yayin da yake magana kan fadar da dakarun Hizbullah din suke yi da ‘yan wadannan kungiyoyi na ta’addanci a kan iyakar kasar Labanon da Siriya kuwa, Sheikh Na’im Qasim ya bayyana cewa dakarun gwagwarmaya suna nan kyam babu wani abin da ya same su yana mai cewa cikin yardar Allah za su ci gaba da riko da wannan tafarki da suka rika ba tare da wata damuwa ko tsoro ba.
Cikin ‘yan kwanakin nan dakarun kungiyoyin ta’addancin Da’esh (ISIS) da Jabhatun Nusra da suke samun goyon bayan kasashe irin su Saudiyya da Qatar da Turkiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila suna ta kokari wajen kutsawa cikin kasar Labanon da nufin kafa sansaninsu don fada da kuma kawo karshen kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah amma har ya zuwa yanzu sun gaza cimma ko da guda daga cikin manufofin na su sakamakon tsayin dakan da dakarun Hizbullah din suka yi lamarin da ya sanya ya zuwa yanzu sun kashe wani adadi mai yawa na ‘yan ta’addan da kuma kame wasu da dama a matsayin fursunonin yaki.
1462654