IQNA

Yahudawan sahyuniya Na Da Burin Ganin An Raba Masallacin Qods

12:44 - October 23, 2014
Lambar Labari: 1463119
Bangaren kasa da kasa, babban limamin masallacin Qods mai alfarma ya bayyana cewa bababr manufar yahudawan sahyuniya it ace fatar ganin an raba wannan masallaci mai albarka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na tashar talabijin ta Palastine cewa, Sheikh Ikrama Sabri babban limamin masallacin Qods mai alfarma ya bayyana cewa bababr manufar yahudawan sahyuniya ita ce fatar ganin an raba wannan masallaci a kan haka ne ma suke tsananta kai hare-harensu a kansa a cikin wadannan lokuta.

Shehin malamain  kuma shugaban kwamitin kare masallacin Qudus ya  yi gargadi akan yadda ‘yan sahayoniya su ke  yi wa alqiblar musulmi ta farko barazana. Shugaban Kwamitin kare masallacin na Qudus.

Sheikh Ikramah Sabri wanda ya yi hira da kafafen watsa labarun Palasdinu ya yi ishara da yadda ‘yan sahayoniyar su ke fakewaa da lokacin bukukuwansu na addini domin muzgunawa musulmi a cikin masallacin na Qudus. Sheikh Ikramah Sabri ya  ci gaba da cewa; Takama da karfi da ‘yan sahayoniyar su ke yi da kuma muzgunawa palasdinawa ba zai taba basu nasarar shimfida ikonsu akan masallacin na Qudus ba.

A cikin kwanakin bayan nan dai ‘yan sahayoniyar suna tsananta kutsawa cikin masallacin na Qudus da kuma takurawa musulmin da su ke salla a cikinsa.

1462933

Abubuwan Da Ya Shafa: aqsa
captcha