Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da taron girmama wadanda suka kwazo a gasar karatun kur'ani mai tsarki wadda aka gudanar kai tsaye ta gidajen talabijin na kasar Mauritanita da ake kira gasar kur'ani ta talabijin a kasar, wadda aka saba yi a cikin 'yan shekaru da suka gabata.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban hukumar kula da ayyukan kur'ani a ma'akatar kula da harkokin addinin muslunci a kasar Sidi Muhammad wold Sheikh shi ne ya jagoranci gudanar da wannan gasa, wadda ta kasance a sahun gaba a cikin ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu a bangaren da ya shafi kur'ani mai tsarki a kasar ta Mauritaniya.
Daga cikin bangarorin da suka gudanar da wannan gasa kuwa hard a dattijai wadanda suka kasance a sahun gaba acikin mahardata na kasar, wadanda kuma sun samu kyutuka na girmama sakamakon kwazon da suka nuna a wanann gasa, da kuma irin hidimar da suka yi kur'ani ami tsarki na tsawon lokaci a rayuwarsu, kamar dai yadda majiyoyin hukumar suka tabbatar da hakan.
Babban dakaraktan hukumar radiyo da talabijin na kasar Mauritaniya ya kasancea wurin a lokacin bayan da kyuatukan, inda ya ya yaba matuka da irin gagarumin ci gaban da wannan gasa ta samu a shekarar bana.