IQNA

Ben Talal Ta Tabbatar Da Cewa Gidan Sarautar Saudiyyah Na Da Hannu Wajen Kafa Daesh

12:57 - October 23, 2014
Lambar Labari: 1463121
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin yayan gidan sarautar Saudiyya ya tabbatar da cewa masarautar kasar tana da hannu kai tsaye wajen kafa kungiyar ta'addanci ta Daesh da aka fi sani da ISIS.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, Walid Bin Talal daya daga cikin yayan gidan sarautar Saudiyya  ya tabbatar da cewa masarautar kasar tana da hannu kai tsaye wajen kafa kungiyar ta'addanci ta Daesh da ke aikata ayyukan ta'addanci a halin yanzu a kan al'ummomin duniya musammana  a yankin gabas ta tsakiya.

Wasu rahotannin sun ce sojojin kasar Iraki sun hallaka 'yan ta'addan kungiyar ISIL guda 30 a yau, tare da kone wasu motoci guda uku da suke dauke da muggan makamai da aka shigo da su cikin kasar ta kan iyakar kasar da Saudiyyah. 
Gidan talabijin na Al-iragqiyyah ya nakalto daga rundunar sojin kasar ta Iraki cewa sojjin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan ne a lokacin da suka shigo cikin kasar ta mashgar saklawiyya daga Saudiyyah dauke da muggan makamai, na fin kaddamar da hare-hare a cikin kasar ta Iraki.
A bangare guda kuma asibin  birnin Karkuk ya sanar da karbar gawawwakin wasu fararen hula 15 a yau da mayakan ISIL suka kashe a cikin wasu kauyuka da ke kusan da yankin, majiyoyin asibitin sun tabbatar da cewa akasarin mutanen da 'yan ta'addan na ISIL suka kashe dai mata ne da kananan yara.
1462963

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya
captcha